1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amirka ta ce ba zata sasanta da ´yan ta´adda ba

January 20, 2006
https://p.dw.com/p/BvBS

Gwamnatin Amirka ta yi watsi da wani tayin neman tsagaita bude wuta da ke kunshe a cikin wani kaset na wani jawabi da aka danganta shi da shugaban kungiyar al-Qaida Osama bin Laden. Kakakin fadar White House ya ce Amirka ba ta shawarwari da ´yan ta´adda, illa iyaka ta yake su. Da farko dai gidan telebijin na Aljazeera ya watsa wani jawabi dake cikin wani kaset wanda aka ce na Bin Laden ne. A cikin kaset din shubaban na Al-Qaida yayi barazanar kai sabbin hare hare akan Amirka, to amma a hannu daya yayi tayin kulla yarjejeniyar dakatar da yaki akan wasu sharudda. Hukumar leken asirin Amirka ta CIA ta tabbatar da sahihancin muryar dake kan kaset din da cewa ta Osama Bin Laden ce. Wanda hakan ya kasance karon farko da aka ji duriyar sa tun bayan watan desamban shekara ta 2004.