Amirka ta ce ba zata iya tabbatar da labarin rasuwar Bin Laden ba | Labarai | DW | 23.09.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Amirka ta ce ba zata iya tabbatar da labarin rasuwar Bin Laden ba

Gwamnatin Amirka ta kasa tabbatar da wani rahoto da wata jaridar Faransa ta buga cewa shugaban kungiyar Al-Qaida Osama Bin Laden ya rasu cikin watan jiya a Pakistan. Wani jami´in yaki da ta´addanci na Amirka wanda ya ki a ambaci sunansa saboda ba´a ba shi umarnin tofa albarkacin bakinsa akan batun ba, ya ce ko da yake ba zasu iya tabbatar da rasuwar Bin Laden din ba, amma ana yada wata kwakkwarar jita-jita game da haka. A yau asabar jaridar Faransa mai suna L´Est Republican ta rawaito hukumar leken asirin Saudiya na cewa bin Laden ya mutu sakamakon zazzabin typhoid. Jaridar ta dogara wannan rahoto na ta da wasu bayanai da ta ce ta samo daga hukumar leken asirin Faransa. A halin da ake ciki gwamnatin Faransa ta fara bincike kan yadda bayanan asirin suka fita.