1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amirka ta ce ba ta mika Saddam ga hukumomin Iraqi ba

December 29, 2006
https://p.dw.com/p/BuW1

Wani jami´in Amirka a Iraqi ya ce ba´a mika tsohon shugaban Iraqi Saddam Hussein ga hukumomin kasar don a zartas da hukuncin kisa akan shi ba. Jami´in wanda ya ki a bayyana sunan sa, ya fadawa kamfanindillancin labarun AFP cewa har yanzu Saddam Hussein na hannun Amirkawa. Wannan furucin na matsayin mayar da martani ga ikirarin da lauyoyin dake kare Saddam Hussein suka yi ne cewa an mika shi ga gwamnatin Iraqi. Da farko kakakin rundunar Amirka ya nunar da cewa ana tsare da Saddam ne a karkashin dokokin gwamnatin Iraqi, amma tsaron lafiyar sa na rataye ne a wuyan dakarun kawance.