Amirka ta ce ba ta da wani shiri na kaiwa Iran ko Syria hari | Labarai | DW | 13.01.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Amirka ta ce ba ta da wani shiri na kaiwa Iran ko Syria hari

Amirka ta musanta jita-jitar da ake yadawa cewa ta na shirin kaiwa kasar Iran ko kasar Syria harin soji. Kakakin fadar White House Tony Snow ya fada a birnin Washington cewa rahotannin na nuni da mummunar fahimtar da aka yiwa jawabin shugaba Bush. A ranar laraba da ta gabata Bush ya zargi kasashen biyu da marawa masu ta da kayar baya a Iraqi baya. Bush ya nunar da cewa zai dauki matakan tsayar da irin wannan taimako.