Amirka ta baiyana aniyar cigaba da shirin kariyar makamai a nahiyar turai | Labarai | DW | 15.06.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Amirka ta baiyana aniyar cigaba da shirin kariyar makamai a nahiyar turai

Sakataren tsaron Amurka Robert Gates yace Amurka zata cigaba da shirin ta na kafa kariyar makamai masu linzami a gabashi turai. A wani taro da ya gudana tsakanin ƙungiyar tsaro ta NATO da kuma Rasha a birnin Brussels, Gates ya shaidawa takwaran sa Rasha Anatoly Serdyukov cewa shawarar da fadar Kremlin ta bayar na yin haɗaka a cibiya guda dake Azerbaijan, matakin cigaba ne amma zai kasance ne kawai ya tallafawa tashar da Amurkan zata kafa a jamhuriyar Czech a ƙasar Poland. Gates yace babu wata ƙasa daga cikin ƙawancen na NATO da ta baiyana adawa da manufar Amurka na kafa kariyar makaman. Ƙasar Rasha na mai raáyin cewa shirin kariyar makaman zai yi barazana ga ainihin nata tsaron. Shugaban ƙasar Vladimir Putin ya buƙaci Amurkan ta sake nazari a game da burin da take da shi na kafa cibiyar kariyar makaman a nahiyar turai.