1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

AMIRKA NA JUYA HANKALINTA GA AFIRKA DON SAMO MAN FETUR

YAHAYA AHMEDApril 14, 2004

Saboda rikice-rikicen da ake yi a Gabas Ta Tsakiya dai, Amirka na kara waiwayawa ga nahiyar Afirka, don samun tabbataccen tushe na man fetur da take bukata. Amma habakar cin hanci da rashawa, da gwagwarmayar da ake yi don mamaye madafan iko, na cikin illolin da ke ta yaduwa a galibin kasashen Afirka masu arzikin man fetur.

https://p.dw.com/p/Bvkh
Mata, a tashar sayad da man fetur a Sao Tome.
Mata, a tashar sayad da man fetur a Sao Tome.Hoto: AP

Yayin da hankalin duniya ya koma kan kasar Rwanda, inda ake juyayin tunawa da cika shekaru goma, tun da aka yi kisan kiyashi a can, a wani yankin Afirkan kuma, an sami barkewar wani mummunan rikici, wanda sakamakon da zai haifar, zai fi ma na Rwandan tsanani. kungiyar nan ta GfbV, mai fafutukar kare hakkin tsirarun kabilu da ke huskantar barazana a duniya ce ta ba da wannan sanarwar. Kamar yadda babban sakatarenta, Tilman Zülch ya bayyanar, kusan mutane miliyan daya ne ke huskantar barazanar yunwa, saboda matakan da gwamnatin Sudan ta dauka na kin kula da addabar da wasu dakarun kabilun Larabawa ke yi wa al’umman yankin Darfur. kungiyar dai ta ce gwamnatin Sudan din ce ma ke daure wa mayakan gindi, inda suke ta yi wa al’umman yankin Darfur da ke yammacin kasar kisan kiyashi. Ma’aikatan ba da taimakon agaji kuma na huskantar matsaloli, saboda shingen da mahukuntan birnin Khartoum ke gindaya musu, kafin su iya kai ga jama’ar da ke bukatar taimako a yankin na Darfur.

Amirka ma ta nuna damuwarta game da halin da ake ciki a yankin. Amma ita Washington, tana magana ne da baki biyu. Ba kare hakkin dan Adam a yankin ne ya fi damunta ba, duk da tawagar da ta tura don ta rarraba wa mazauna yankin da rikicin ya shafa kayayyakin agaji. baBu shakka, ita Amirkan na sha’awar ganin cewa an sami kwanciyar hankali a Sudan. Amma kare maslahar kamfanoninta masu hakon man fetur a kasar, shi ne abin da ya fi damunta. Ba a Sudan din kadai ne kuwa take harkar man fetur din ba. Kamar yadda cibiyar nan ta Center for Strategic and International Studies da ke birnin Washington ta bayyanar, Amirka yanzu tana ba da karfi ne a Tsakiya da kuma Yammacin Afirka, don ganin cewa ta rage dogarar da take yi kan samo man fetur da take bukata daga yankin Gabas Ta Tsakiya, inda yake-yake da rikice-rikice ke ta kara habaka.

Kamfanonin hakon man fetur dai, na ganin cewa kafin shekara ta 2010, daga Afirka ne Amirka za ta dinga samo kusan kashi daya bisa hudu na man fetur din da take bukata. Tuni dai za a iya lura da yadda manyan kamfanonin Amirka kamarsu Exxon Mobile, suka kafu sosai a Yammacin Afirka. Suna hako mafi yawan mansu a nan ne daga cikin teku, abin da ke sa ba sa damuwa da yake-yaken basasa ko kuma wasu rigingimun da ake yi a kasashen da suke aikin. A halin yanzu dai, Amirkawa na ta kara zuba jari ne a wannan yankin na Yammacin Afirka, inji Antonie Ford, shugaban sashen Afirka na gidauniyar Heirich-Böll, a cikin wata fira da ta yi da gidan rediyon Deutsche Welle kan wannan batun.

A lal misali ana iya ganin karin yawansu a kasar Equitorial Guinea, inda ba da dadewa ba ne aka gano dimbin yawan gurbataccen man fetur.

Amma a galibi, arzikin man fetur din, wani sabon bala’i yake janyo wa kasashen na Afirka. Inda da babu wani rikici, sai ka ga har yake-yaken basasa ake yi bayan an gano man fetur. Antonie Ford dai, ta bayyana cewa, wani karamin nau’i na al’umman kasashen ne ke cin moriyar arzikin man da aka gano ko kuma ake haka. Mafi yawan jama’a, sai wahalhalu kawai suke ta kara huskanta. Ta dai ba da misalin Najeriya, inda ta ce, kusan kashi 70 cikin dari na kudaden shigarta daga kasuwancin man fetur suke. Amma fiye da kashi 60 cikin dari na al’umman kasar ne ke ta fama da talauci.

A tsibirin Sao Tome kuma, `yan tawayen da suka yi yunkurin juyin mulki a shekarrar bara, sun ce hana al’umman kasar cin moriyar albarkar da ake samu daga man fetur din ne dalilin da ya sa suka yi kokarin kifad da gwamnati.

Kamfanonin hakon man ma na da nasu laifin. Sau da yawa su ne ke bai wa mahukuntan kasashen da suke, makudan kudade na cin hanci da rashawa, don su iya yin yadda suka ga dama da harkar man, ba tare da wani ya bincike su ba.

An dai sha yin kira ga kamfanonin da su bayyana duk irin kudaden da suke kashewa a harkokin hakon man a fili. Wasu kamfanonin kamarsu Shell da BP, sun amince su goyi bayan wannan shirin. Amma kamfanin Exxon Mobile na Amirka, ya ce ko daya ba zai taba bayyana harkokinsa a bainar jama’a ba.