Amirka na girmama addinai daban-daban
August 14, 2010Shugaban Amirka Barack Obama ya baiyana amincewar sa da gina wani masallaci a birnin New York ta Amirka. A wani jawabi a lokacin cin abincin buɗe baki da wasu Amirkawa musulmai a fadar white House, Obama ya bayyana yancin da kowace al'uma keda ita na gudanar da addini ba tare da tsangwama ba, kamar dai yadda yake ƙunshe a kundin tsarin mulkin Amirka shekara da shekaru.
Obama yace- Amirkawa munyi imani da 'yancin addini. kuma kowa yana da 'yancin gudanar da addinin sa, a wannan ƙasa ba tare da tsangwama ba, don haka gwamnatin mu ba za ta nunawa kowa ban-banci ba.
Tuni dai masu suka ga matakin gina masallacin da kuma makarantar Islamiya a kusa da harabar da aka kai harin 11 ga watan satumba, suka baiyana kalaman na shugaba Obama da cewar cin fuskane ga wayan da suka rasa rayukan su a harin na birnin New York.
Mawallafi: Babangida Jibril
Edita: Abdullahi Tanko Bala