Amirka na aike wa Isra’ila da makamai cikin gaggawa. | Labarai | DW | 23.07.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Amirka na aike wa Isra’ila da makamai cikin gaggawa.

Kafofin yaɗa labarai a birnin Washington sun ruwaito cewa, Amirka ta fara aike wa Isra’ila da wasu bamabamai na musamman, a daidai lokacin da take kai farmaki a Lebanon. Wani jami’in gwamnatin Amirkan, wanda ya bukaci kada a ambaci sunansa, ya faɗa wa kamfanin dillancin labaran APF cewa, tsain da shawarar aikewa da makaman ya biyo bayan wata bukata ne da Isra’ilan ta miƙa wa birnin Washington, kuma an yi hakan ne ƙarƙashin wata yarjejeniyar bai wa Isra’ilan makamai da aka cim ma tun shekarar bara. Jami’in dai ya ƙara da cewa an aike da makaman, ko kuma an kusa miƙa su ga Isra’ilan, amma bai ba da ƙarin haske ko ta jirgin ruwa ko kuma ta sama ne aka yi jigilar makakan ba.