1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amirka: Mace ta zama shugabar hukumar CIA

Ramatu Garba Baba
May 18, 2018

An nada Gina Haspel shugabar hukumar leken asirin Amirka ta CIA bayan da majalisar dattijan kasar ta kada kuri'u don amincewa da nadin. Haspel ta kasance mace ta farko da aka zaba don rike wannan mukami a kasar.

https://p.dw.com/p/2xv3W
USA Gina Haspel, designierte CIA-Direktorin | Anhörung Senate Intelligence Committee in Washington
Hoto: Reuters/K. Lamarque

 

An sami sabanin ra'ayi bisa nadin matar mai shekaru sittin da daya a sanadiyar zarge-zarge da ake ma ta na gallazawa wasu mutane da aka tsare bayan munmunar harin da aka kai wa Amirka na 9/11 a shekarar 2001.

Shekaru akalla talatin da uku ta kwashe tana aiki a karkashin hukumar kafin wannan mukami, ta kuma maye gurbin Mike Pompeo wanda shi ne sakataren harkokin wajen Amirka a yanzu. Bayan da aka amince da nadin Haspel, kungiyar kare hakkin bil adama ta Human rights ta fidda sanarwa inda ta soki matakin bai wa matar da ta ce ta aikata laifi da keta haddin bil'adama.