1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amirka: Kalubalen mallakar bindiga

Abdourahamane Hassane
March 25, 2018

Sama da mutane miliyan daya ne galibi matasa suka gudanar da zanga-zanga a garuruwa daban-daban domin ganin gwamnatin Amirka ta sake yin lalle a kan batun mallakar bindiga.

https://p.dw.com/p/2uvyW
USA "March for Our Lives"
Hoto: REUTERS

A birnin New York akalla mutane dubu 175 suka fantsama a kan tituna a kan taken da aka yi wa gangamin ''mu yi tattaki don rayuwarmu.'' Hakan kuwa ya biyo bayan kisan 'yan makaranta 17 da wani dan bindigar ya yi a cikin wata makaranta a Florida.