Amirka ka iya zama kan teburin shawarwari da Iran | Labarai | DW | 12.09.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Amirka ka iya zama kan teburin shawarwari da Iran

Sakatariyar harkokin wajen Amirka Condoleezza Rice ta ce Amirka ka iya shiga cikin tattaunawar da ake yi da Iran, idan gwamnati a Teheran ta dakatar shirinta na nukiliya na wucin gadi. Kalaman na Rice na matsayin wani sassauci akan matsayin Amirka dangane da shirin nukiliyar Iran. Da farko Amirka ta ce tana neman kwamtin sulhun MDD ya kakabawa Iran takunkumi saboda kin dakatar da aikin sarrafa sinadarin uranium. A kuma halin da ake ciki babban jami´in dake kula harkokin ketare na KTT Javier Solana da mai shiga tsakani na Iran Ali Larijani sun ce sun samu ci-gaba a tattaunawar da suka fara a karshen mako da nufin kawo karshen fito na fiton da ake yi game da muradin Iran na mallakar fasahar nukiliya. Wani jami´in diplomasiyar kungiyar EU ya ce Larijani ya gabatar da tayin dakatar da aikin inganta uranium na tsawon watanni biyu a gun shawarwarin da suka yi a birnin Vienna da aka ce yayi armashi.