1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amirka: Dan bindiga ya kashe mutane sama da 50

Gazali Abdou Tasawa
October 2, 2017

A kasar Amirka mutane sama da 50 ne aka tabbatar sun halaka ya zuwa yanzu a sakamakon wani hari da wani dan bindiga ya kai a wani bikin kida da waka a birnin Las Vegas.

https://p.dw.com/p/2l6pr
USA - Schießerei in Las Vegas - Polizeieinsatz
Hoto: Getty Images/E. Miller

A kasar Amirka mutane sama da 50 ne aka tabbatar sun halaka ya zuwa yanzu a sakamakon wani hari da wani dan bindiga ya kai a wani wurin bikin kida da waka a birnin Las Vegas. Daga hawa na 32 na benen wani Hotel ne dan bindigar ya yi harbin kan mai uwa da wabi a kan 'yan kallo da suka tattaru a wajen bikin kidan. 

Sai dai jami'an 'yan sanda sun bindige mutuman mai suna Stephen Paddock mai shekaru 64 wanda kwamishinan 'yan sanda na birnin na las Vegas wato Joe Lombardo ya ce sun iske tarin bindigogi a dakin da ya ke zaune a cikin Hotel din na Mandalay Bay. Hukumar 'yan sandar ta kuma ce akwai wasu mutanen sama da 200 da suka ji raunia  cikin harin.

Kawo yanzu dai ba a kai ga samun bayanai kan dalillan mutuman na kai wannan hari ba, amma kuma tuni hukumar 'yan sanda ta soma bincike a kai