Amirka da Turkiyya sun sasanta kan Visa
November 6, 2017Talla
Wannan matakin sassauta matakai na musanyar samun damar shiga kasashen biyu na zuwa ne kwana guda bayan ganawar Firaiministan Turkiyya Binali Yildirim a birnin Washington, tare da mataimakin shugaban kasar Amirka Mike Pence. A baya dai Yildirim ya nuna takaici kan irin tsamin dangantaka da ke tsakanin kasashen biyu ke shafar harkokin diflomasiya.
Kasashen Turkiyya da Amirka da ke zama mambobin kungiyar tsaro ta Nato, sun kasashece cikin takun saka bayan da hukumomin Turkiyya suka rika kame 'yan Amerika da ke shiga kasar bisa zargin alaka da kungiyar malamin addininnan dan aksar Turkiyya da ke samun mafaka a Amirka, malamin da gwamnatin shugaba Raccep Tayyib Erdogan suka daura alhakin yunkuri juyin mulki a shekarar 2016.