1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amirka da Najeriya za su yaki ta'addanci

Ubale Musa/PAWJuly 21, 2015

Kasashen biyu sun sami matsala a baya, inda Najeriya ta zarge ta da leka mata asiri ita kuma Amirkar ta ce babu gaskiya a yakinta da Boko Haram, amma yanzu sun daidaita.

https://p.dw.com/p/1G2CK
USA Muhammadu Buhari und Barack Obama in Washington
Hoto: Getty Images/A. Wong

Tuni dai wata ziyarar da shugaban Najeriyar ke yi a kasar Amirkan ta fara nuna alamun da da mai ido bayan da Amirkan ta baiyana aniyarta ta tallafawa kasar ya zuwa kai karshen yakin. Duk da cewar dai ya zuwa yanzu babu cikkaku na bayanai na tallafin dai, gamsuwar Amirka ga irin dabarun sabuwar gwamnatin ta Abuja dai na zaman alamun farko na irin nisan tafiya a tsakanin kasashen biyu da a baya suka yi rabuwar baram-baram bisa matsalar yakin.

Tun da farkon fari dai Amirkan ta bada agaji na dalar Amurka miliyan kusan biyar ga sabuwar rundunar hadin gwiwar tafkin Chadi a farkon watan Yulin da mu ke ciki a wani abun da ke zaman alamun bude sabon babi na tabbatar da kai karshen matsalar a cikin sauri. Tallafin kuma da ke iya kara karuwa a tunanin Dr Sadiq Abba da ke zaman masanin harkoki na siyasa a Jami'ar da ke nan birnin tarraya ta Abuja.

Mafita ga yunkurin sabuwar gwamnati na yaki da Boko Haram

A baya dai Amirkan ta yi ta toshe kafafen na Abuja ga batun sayen makaman da a a cewar birnin na Washington ba za ta bayar ba kada ya kare a hannun Boko Haram, ko kuma a yi amfani da shi wajen cin zarafi na fararen hula a bangaren sojoji. Abun kuma da ya tilastawa Najeriyar tafiya ta baya na fage da nufin cika burinta na samar da makamai.

A zahirance dai ita kanta mai bada taimakon, har yanzu tana fafatawa a kasashe irin su Afganistan da Iraki, da nufin tabbatar da karshen ta'addancin da ke zaman ruwan dare gama duniyar Allahu, abun kuma da ya sa wasu ke tunanin da kamar wuya duk wani agaji na Amirkan ya tabbatar da kai karshen matsalar da ta share shekara da shekaru ta kuma gagari kundila na cikin sojan kasar ta Najeriya a halin yanzu. To sai dai kuma a tunanin Husaini Monguno da ke zaman masani kan harkoki na tsaro, Buharin ba shi da zabin da ya wuce hada hannu da Amirkan in har yana da bukatar cika alkawarin da ya dauka yayin yakin neman zabe.

USA Muhammadu Buhari und Barack Obama in Washington
Hoto: Reuters/K. Lamarque

Abun jira a gani dai na zaman samar da dabarun tunkarar makamin karshe dake hannu a kun giyar a halin yanzu da kuma ke zaman amfani da yara kanana da nufin kuna ta bakin wake ga farar hula, a cikin yakin da ya kalli hare hare kusan 25 na bakin waken dama asarar ta rayuka sama da 600 a farkon makonni shida na gwamnatin ta Buhari.