Amirka da Katar za su yaki ta'addanci
July 11, 2017Talla
Firaiministan Katar Sheikh Mohammed bin Abdulrahman Al-Thani, ya nuna gamsuwa kan rawar da Amirkan ke takawa na shiga tsakanin ta da sauran takwarorinta da suke takun saka. A yanzu dai Katar ce kasa ta farko a daular larabawa da suka cimma yarjejeniya mai karfi da Amirka na aza tubalin yakar tsauraran akidu da ayyukan ta'addanci.
A farkon makonnanne sakataren Amirka Rex Tillerson ya fara ziyarar rangadi a kasashen yankin larabawa, da nufin shiga tsakanin rikicin kasashen bisa zargin tallafawa ta'addanci da ake wa Katar kallo da shi.