Amirka da Japan sun gargaɗi Korea Ta Arewa da ta soke gwajin makamai masu linzamin da take niyyar yi. | Labarai | DW | 18.06.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Amirka da Japan sun gargaɗi Korea Ta Arewa da ta soke gwajin makamai masu linzamin da take niyyar yi.

Amirka da Japan, sun gargaɗi ƙasar Korea Ta Arewa da ta guji gudanad da gwajin makamai masu linzamin nan da take niyyar aiwatarwa, waɗanda ake fargabar cewa, za su iya lulawa har zuwa Amirka. Ministan harkokin wajen Japan, ya ce idan makaman suka faɗo a kan harabar ƙasarsa, to birnin Tokyo za ta ɗau lamarin ne tamkar hari Korea Ta Arewan ta kai mata.

Wani kakakin ma’aikatar harkokin wajen Amirka kuma, ya ce gwajjin makaman dai tsokana ce da Korea Ta Arewan ke son yi wa maƙwabtanta, kuma ya yi kira ga mahukuntan birnin Pyongyang da su koma kan teburin shawarwari don tattauna batun makaman nukiliyanta. A cikin shekarar 1998 ma, sai da Korea Ta Arewan ta yi gwajin wasu makamai masu linzamin, waɗanda ta ce rokoki ne na tura tauraron ɗan Adam zuwa sararin samaniya.