1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amirka da Faransa sun samu ci-gaba akan kudurin Libanon

August 5, 2006
https://p.dw.com/p/Bunl

Kasashen Amirka da Faransa sun samu ci-gaba a kokarin da suke yi na cimma yarjejeniya kan wani kuduri game da GTT, to amma har yanzu ba su cimma wata masalaha ba. Wani kakakin ma´aikatar harkokin wajen Amirka ya nunar da cewa sassan biyu sun kusan kusantar juna game da wani daftarin kuduri na bai daya. Jami´an diplomasiya sun ce ana samun sabani ne game da ka´idojin girke dakarun kiyaye zaman lafiya na kasa da kasa a Libanon. Wani batun da ake takaddama akai shi ne bukatar da Isra´ila ta gabatar na kasancewar dakarunta a cikin Lebanon. A kuma halin da ake ciki babban sakataren MDD Kofi Annan da shugaban Amirka GWB sun tattauna ta wayar tarho akan halin da ake ciki a yankin GTT, to amma ba´a ba da karin bayani ba.