Amirka da Faransa sun amince da kalaman wani kuduri kan Libanon | Labarai | DW | 05.08.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Amirka da Faransa sun amince da kalaman wani kuduri kan Libanon

Kasashen Amirka da Faransa sun cimma yarjejeniya akan wani kudurin kwamitin sulhu na MDD da nufin kawo karshen fadan da ake yi tsakanin Isra´ila da ´yan yakin sunkurun Hisbollah a kudancin Libanon. Kuduri zai yi kira da a tsagaita wuta kwata-kwata to amma bai tsayar da lokacin yin haka din ba. Wasu majiyoyi sun nunar da cewa kuduri zai bawa Isra´ila damar mayar da martani ga hare haren ´yan Hisbollah. Jami´an diplomasiyar na Faransa da Birtaniya sun ce nan da sa´o´i kalilan kwamitin sulhu zai yi zama na musamman don yin nazari akan kalmomin da aka yi amfani da su a cikin kudurin. Jakadan Amirka a MDD John Bolton ya ce yana sa rai za´a amince da kudurin a cikin kwanaki kadan masu zuwa.

Bolton ya ce: "Mmuna sa rai manyan kwararru zasu gana don amsa tambayoyi kuma a shirye muke mu ci-gaba da aiki gobe don amincewa da kudurin. Yanzu haka dai mun cimma yarjejeniya kuma a shirye muke mu ci-gaba.”