1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amirka cikin halin tsaka mai wuya a Afghanistan

August 10, 2010

Sabuwar muhawara a Amirka game da zaman sojojin kasar a Afghanistan

https://p.dw.com/p/OhiT
Mayakan Taliban da makaman suHoto: AP

Tashoshin Television na Amirka sun dauki lokaci mai tsawo suna nuna hotunan wani likitan idanu da likitan hakora yan kasar wadanda suke daga cikin wadanda aka kashe a kasar ta Afghanistan. Dangane da haka, sakatariyar harkokin wajen Amerika, Hilary Clinton take bayani da cewa:

"Aiyukan wannan tawaga basu wuce na taimakon jama'a ba tare da sun dogara da gwamnati ko wata alaka da addini, ko neman jan hankalin mazauna yankunan da suke ya zuwa ga wani addini ba. Biyu daga cikin likitocin na Amerika sun yi fiye da shekaru 30 suna aiki a Afghanistan. Sun taimaka wa yan Afghanistan tun a zamanin da sojojin Soviet suka mamaye kasar da kuma a zamanin da yan kungiyar Taliban suka tafiyar da mulki a wnanan kasa".

Clinton ta kara da cewar karfin zuciyar su da tausayin su ga yan Afghanistan tare da siyaiyar wadada aka kashe ga al'ummar Afghanistan duka zasu sanya Amirka ta kara kwazo a matakan ta kan kasar.

To sai dai idan aka yi maganar Afghanistan, babban abin da kan dauki hankalin Amirkawa shine tambayar shin yanzu me ya kamata ayi? Shin yanzu ina aka dosa? Wasu rahotanni kimanin dubu 70 na asiri da shafin Internet mai suna Wikileaks ya gabatar dangane da zaman sojojin Amirka da aiyukan su a Afghanistan, sun kara jefa gwmanatin Amirka cikin mawuyacin hali, game da neman kawo karshen yakin da bisa dukan alamu ba zata sami nasarar sa ba a kasar ta Afghanistan. Kisan gilla da aka yiwa tawagar ta mutane goma, ya kuma kara nunar da yadda ake ci gaba da fama da rashin kwanciyar hankali a yankuna da dama na kasar, duk kuwa da kasancewar sojojin Amirka fiye da dubu 100 a can. Bayan yaki na fiye da shekaru takwas da sojojin Amirka fiye da dubu ukku da aka kashe, yanzu lokaci yayi da Amirka zata janye, a bisa ra'ayin yan jam'iyar democradiya da dama. Wani dan siyasa ma yayi tambayar:

"Shin me zai faru ne idan mu Amirkawa muka janye daga Afghhanistan"

Wannan tambaya ce da babu sauran a kauce mata, musamman tun bayan mujallar Time a shafin ta na farko farko ta buga hoton wata yar shekaru 19, Bibi Aisha daga Afghanistan, wadda mijinta ya yanke mata hanci da kunne, wanda kuma in da sojojin Amerika basu taimaka ba, da ta rasa ranta, saboda dangin ta dake tsoron yan kungiyar Taliban sun ki kawo mata dauki.

Masu goyon bayan kiran Amirka ta janye sojojin nata, sun yi korafin cewar gwmanatin Amirkan tana amfani da wannan hali Bibi Aisha ta shiga, domin kampe na jan hankalin ci gaba da zaman sojojin Afghanistan. Amirka, inji masu neman ta janye, ba ta shiga Afghanistan ne da nufin ta tabbatar da kare yankin mata da ganin yan mata sun sami ilimi ba. Sai dai wnanan ba shine ra'ayin sakatariyar harkokin wajen Amirka Hilary Clinton ba.

"Yan Taliban sun sha zubawa yan mata gubar dake lalata fuskokin su, lokacin da suke kan hanyar zuwa makarantu".

Hakan inji ta, ya nuna zahirin abin da zai faru, idan har Amirkawan suka gaggauta janyewar su daga Afghanistan, suka mika mulkin da zai fada a hannun yan Taliban, inda har ma ta tuna cewar a baya-bayan nan ne yan Taliban din suka zargi wani yaro dan shekara bakwai da laifin leken asiri suka kuma rataye shi.

Tace tilas ne mu ci gaba da gwagwarmaya a Afghanistan da karin sojoji, ko da shike tana sane da cewar wannan yaki yana iya jawowa shugaba Barack Obama ya rasa samun nasarar kokarin a zabe shi a wa'adi na biyu idan ya nema.

Mawallafi: Umaru Aliyu

Edita: Muhammed Nasiru Awal