Amirka ba za ta bai wa Saudiyya makamai ba | Labarai | DW | 14.12.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Amirka ba za ta bai wa Saudiyya makamai ba

Baraka tsakanin kasar Amirka da Saudiyya ta fito fili bayan da Amirkar ta ce ta daina bai wa Saudiyya makamai saboda damuwa kan yakin Yemen

Amirka ta dakatar da baiwa Saudiya wasu makamai bayaan da ta fusata da yawan hasarar rayukan fararen hula sakamakon luguden wutar da Saudiyyar ke yi Yemen.

Wani babban jami'in gwamnatin Amirkan ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa gwamnatin ta damu da yadda Saudiyya ke aiwatar da yakin kan yan tawayen Houthi.

Wannan matakin dai ya kara fito al'amura fili dangane da sabanin da ke tsakanin kasashen biyu aminan juna. Saudiyyar dai ba ta maida martani kan matakin ba, kawo yanzu.