1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amirka ba ta azabtar da wadanda take zargi da aikata laifi

October 28, 2006
https://p.dw.com/p/Bue7

Shugaban Amirka GWB ya jaddada matsayin sa cewar gwamnatin Amirka ba ta amince da wani mataki na azabtarwa ba. hakan ya zo ne bayan kalaman da mataimakin shugaban Amirka Dick Cheney yayi a wata hira da aka yi da shi inda ya ce nitsad da mutanen da ake zargi da aikata ta´addanci zai taimaka wajen samun bayanai daga garesu. Kungiyoyin kare hakin bil Adama sun yi ikirarin cewa kalaman na mista Cheney tamkar nuna amincewa ne da da amfani da wata dubara inda ake yiwa mai laifin barazanar nitsa da shi a ruwa. A martanin daya mayar shugaba Bush cewa yayi.

“Gwamnatin Amirka ba ta azabtar da wadanda ake zargi da aikata laifi, muna yi musu tambayoyi ne don samun bayanai daga garesu, wadanda zasu taimaka mu kare kasar mu.”