Amincewa da shirin tallafawa bankuna | Siyasa | DW | 02.10.2008
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Amincewa da shirin tallafawa bankuna

Da gagarumin rinjaye majalisar dattijan Amirka ta amince da shirin ceto bankuna na dala miliyan dubu 700 bayan an sake yi masa fasali.

default

Shugaban masu rinjaye a majaliar dattijan Amirka Harry Reid, a taron manema labarai

A matakin farko shirin ya tanadarwa gwamnati sayen kadarorin bankuna da darajarsu ta faɗi. Yanzu dai ana sa rai majalisar wakilai za ta bi sahun ta dattijan wajen amincewa da shirin a ƙuri´ar da za ta kaɗa a gobe Juma´a.


Da waɗannan kuɗaɗe dai da gwamnatin Amirka za ta iya bawa kowane ɗan ƙasar kyautar dala 6000 ko sayen man fetir ga kowane mai mota a ƙasar har tsawon shekara ɗaya da rabi, to sai dai za ta yi amfani da kuɗi dala miliyan dubu 700 don cin wasu sababbin basussuka. Bayan fatali da shirin da majalisar wakilai musamman ´yan ɓangaren jam´iyar Republicans ta shugaba George W Bush suka yi a ranar Litinin, shugaban ya sake yin kira ga majalisar da ta amince da shirin tallafin cikin gaggawa.


Ya ce: "Yana da muhimmanci wakilan majalisar su ɗauki wannan dokar da muhimmanci domin dole harkar ba da bashi ta farfadɗo ta yadda ƙananan kamfanoni za su ci-gaba da samun kuɗin tafiyar da harkokinsu."


Da rinjayen ƙuri´u 74 kan 25 ´yan majalisar dattijan sun amince da shirin tallafawa bankunan da dala miliyan dubu 700 bayan an yi masa kwaskwarima.


A zaman kaɗa ƙuri´ar hankali ya fi karkata kan sanatoci biyu wato John McCain da Barack Obama waɗanda dukkansu biyu ke takarar neman shugabancin Amirka ƙarƙashin inuwar jam´iyunsu. Kasancewarsu a majalisar a lokacin kaɗa ƙuri´a na da muhimmanci ga yaƙin neman zaɓe, kuma dukkansu biyu sun goyi da bayan wannan shirin, to sai dai Barack Obama na jam´iyar Democrat ne kaɗai ya fito ƙarara ya yi magana gabanin kaɗa ƙuri´ar.


Ya ce: "Muna buƙatar wani kwamiti mai zaman kansa wanda zai sa ido tare da bin diddigin wuraren da za a kashe waɗannan kuɗaɗe. ba za mu iya taimakawa bankunan kaɗai ba tare da miƙa hannun taimakonmu ga miliyoyin magidanta waɗanda suka shiga halin ni ´ya su sakamakon wannan matsala a kasuwannin hada-hadar kuɗi ba."


A cikin dokar dai wadda majalisar dattijan ta amince da ita an ware dala miliyan dubu 250 don rage basussukan banki nan take, sannan sauran za a riƙa bayarwa kashi kashi.


A cibiyoyin hada-hadar manyan bankunan a nan Turai farashin hannayen jari ya ɗan farfaɗo a farkon hada-hadar cinikaiya da safiyar yau ɗin nan sakamakon amincewa da shirin ba da tallafin da majalisar dattijan Amirkar ta yi. To sai dai a Tokyo saɓani haka aka gani inda farashin hannun jari ya faɗi da misalin kashi 1.4 cikin 100 a kasuwar Nikkei ta babban birnin na ƙasar Japan.