1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amfanin hanyoyin sadarwa na zamani ga tattalin arziki Afirka

February 27, 2017

Wakilai daga kasashen Afirka na halarta wani taro na masu yin amfanin da hanyoyin sadarwa na zamani domin duba tasirin da suke da shi wajen ci gaban tattalin arziki Afirka.

https://p.dw.com/p/2YKPn
Elfenbeinküste Symbolbild Handynutzung
Hoto: Getty Images/AFP/I. Sanogo

Wannan dai shi ne karo na biyar da birnin Lagos na Nigeria ke karbar ragamar gudanar da taron wanda ya hada wakilai daga kasashe sama da 40 daga nahiyar  Afirka.Shafuka dai na sada zumunta irinsu Facebook,daTwitter,da sauransu na taka muhimmiyar rawa wajen ci gaban tattalin arziki a Afirka.A baya dai a Najeriyar sai da majalisar kasa ta so ta daukar wata doka ta haramta amfani da labarai da ba su da tushe amma hakan bai yi nasara sakamakon yadda kungiyoyi masu fafutuka suka dage wajen nuna irin tasirin da shafukan ke da su wajen samun ci gaba.

A na sa ran wannan taro zai kara duba irin matsalolin da ake fuskanta wajen yin aiki da shafukan sada zumunta, wanda ko'ina a yanzu  suka zama ruwan dare kama duniya,wanda kuma ake yin amfanin da su wajen gudanar d hrkokin kasuwanci na yau da kullum.