1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya-Amfani da mata wajen kai hari

Al-Amin Sulaiman MuhammadJanuary 12, 2015

Kungiyoyin masu fafutukar kare hakkin mata da masana tsaro a Najeriya sun bi sahu wajen tofa albarkacin bakinsu kan karuwar hare-haren kunar bakin wake da mata ke kaiwa a wasu sassan kasar.

https://p.dw.com/p/1EJ3C
Hoto: picture alliance/abaca

Hare-Haren kunar bakin wake da ake zargin ‘yan mata na kaiwa a sassan arewacin Najeriya lamarin da ke ci gaba da haifar da fargaba tsakanin al'ummar yankin ya ja hankulan kungiyoyin kare hakin mata da masana tsaro wanda suka bayyana shi a matsayin sabon yanayi mai cike da ban tsoro. Na baya-bayan nan shi ne wanda aka kai a karshen makon da ya gabata inda sama da mutane 30 suka riga mu gidan gaskiya sanadiyyar wasu jerin hare-hare da ake zargin wasu ‘yan mata sun kai a jihohin Borno da Yobe. A cewar wani masanin al'amuran tsaro a Najeriya kaftin Yelwaji Babbaji mai ritaya wannan wani sabon yanayi ne da a baya ba san shi a wannan sashi na duniya ba.

Nigeria Anschlag 28.11.2014
Hoto: Reuters

A 2014 mata suka fara kai hari a Najeriya

A farkon watan Disambar shekara da ta gabata ta 2014 ma dai sama da mutane 50 ne suka mutu a wasu tagwayen hare-haren kunar bakin wake da wasu mata suka kai a babar kasuwar garin Maiduguri da aka fi sani da 'Monday Market.' Haka kuma a baya an kai wasu hare-haren kunar bakin wake na ‘yan mata a garuruwan Kano da Azare a jihar Bauchi da kuma Gombe da suma aka samu asarar rayuka tare da jikkatar mutane da dama. Ko yaya kungiyoyin kare hakkin mata ke kallon wannan hare-hare da ‘yan mata ke kaiwa? A cewar Dr Elisa Danladi shugabar kungiyar kare hakkin mata da kula da bunkasar su da aka ke kira da 'Development Initiative for African Women' wannan sabon salo abin takaici ne kuma suna bakin ciki da faruwar lamarin matuka.

Wadannan ‘yan mata da ke zaune cikin al'umma suna kuma yawo a tsakanin mutane ba su da kamanni ko alamu da za'a iya gane su abin yake ba su damar samun nasarar kai hare-haren a lokuta da dama. Ko me ke sa ana amfani da irin wadan nan ‘yan mata don kai harin kunar baki wake? Dr Elisa Danladi ta ce a ganinta saboda an yadda da mata kuma ba a zarginsu da aikata muggan laifuka kamar wannan.

Nigeria Anschlag ARCHIVBILD 19.05.2014
Hoto: picture-alliance/AP Photo

Ba a zargin mata da kokarin aikata laifi

Wannan ma kuma shine tunanin masana tsaro kamar yadda kaftin Yelwaji Babbaji mai ritaya ke cewa mata na tsakanin al'umma kuma ba ai musu tunanin aikata kisan kai. Wadan nan hare-haren kunar bakin wake da ‘yan matan ke kaiwa sun fara sauya tunain al'umma musamman kan ‘yan mata inda a wasu wuraren ma ake samun tsangwamar wasu da ba su san hawa ba bare sauka.