1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amfani da makamai masu guba a Siriya

Zainab Mohammed Abubakar
April 6, 2017

Kasashen yammaci na Turai sun gabatar wa kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniya daftarin neman binciken amfani da makamai masu guba kan fararen hula a Siriya

https://p.dw.com/p/2aoEO
Syrien Idlib Giftgasangriff
Hoto: picture-alliance/abaca/S. Zaidan

Ministan harkokin waje na kasar Siriya Walid al-Moallem ya karyata zargin da ake wa dakarun gwamnati na amfani da makamai masu guba a gundumar Idlib. Ya na martani ne dangane da zargin da ake wa Siriya na amfani da makamai masu guba da yayi sanadiyyar mutuwar mutane masu yawa daura da raunata wasu.

Kasashen yammaci na Turai da Amurka da hukumomin lafiya na ci-gaba da yin Allah wadai kan wadanda ke da alhakin amfani da gubar akan fararen hula. Amurka da Faransa da Birtaniya sun gabatar kwamitin MDD daftarin doka da ke bukatar gudanar da bincike kan batun.

Ministan harkokin wajen Birtaniya Boris Johnson da ya bayyana takaicinsa, ya jaddada bukatar daukar matakan hukunci akan wadanda suka aika laifin.

" Da farko dai ya zamanto wajibi a yi Allah wadan wannan lamari a matakin kasa da kasa. Dole ne mu bi diddigin wannan batu. Ban san dalilin da zai sa wani a komitin sulhu zai ki rattaba hannu akan kudurin da zai yi Allah wadan gwamnatin Siriya ba".