Ambaliyar ruwa ta tsananta a wasu jihohin Amurka
January 2, 2006Talla
Ana ci gaba da ruwa kamar da bakin kwarya kwanaki biyu jere da ya janyo ambaliyar ruwa a arewacin Kalifonia na kasar Amurka.
Hakazalika a yankin St Helena ruwan saman ya sanya kogin Napa yayi amabaliya wadda ya tilastawa wasu jamaa kusan 100 suka tsere daga yankin.
A yankunan jihohin Oklahoma ,Texas da New Mexico kuma wutar daji na ci gaba da ruruwa inda akalla aka sanarda irinsa kusan 20 a yankin Texas kadai,hakazalika a yammacin Dallas wutar dajin na barazana ga kusan gidaje 200 a yanikn.