Ambaliyar ruwa a Togo | Labarai | DW | 13.09.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ambaliyar ruwa a Togo

Ruwan sama kamar da bakin ƙwarya a ƙasar Togo, sun hallaka mutane 20, tare da jikkata wasu da dama a jihar Kpendjal, dake tazara kilomita 650, a arewancin Lome baban birnin ƙasar.

A wata sanarwa da ta hiddo, gwamnatin ƙasar ta bayana cewar gidaje dubu 22 su ka rugurguje sannan mutane kimanin dubu 40 su ka rasa matsugunai a sakamakon wannan ambaliya.

Kazalika, ruwan sun share dubbunan ekoki na gonaki, tare da kada gadoji da makarantu na karkara masu yawa.

Gwamnati ta bayyana ware kuɗi milion ɗari 5 na CFA domin kai agaji ga mutanen da ambaliyar ta rutsa da su.

Ita ma ƙasar France, ta aika jiragen sama 2, masu dura angulu, don ci gaba da ceton jama´a.

Domin nuna alhini ga wanda su ka rasa rayuka, gwamnati ta umurci yin zaman makoki na kwanaki 3 a fadin ƙasar baki ɗaya.