1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ambaliyar ruwa a Koriya ta Arewa ta halaka daruruwan mutane

July 21, 2006
https://p.dw.com/p/Bupo
Hukumomi a kasar KTA sun ce daruruwan mutane sun mutu ko kuma sun bata sakamakon rashin kawo yanayi a wannan kasa mai bin tsarin kwaminisanci. Kamar yadda kamfanin dillancin labarun kasar wato KCNA ya nunar, ruwan sama da ake yi kamar da bakin kwarya ya lalata dubban gidaje da gine ginen gwamnati da hanyoyin mota da kuma na dogo. A kuma halin da ake ciki yawan mutanen da suka rasu a ambaliyar ruwa da kuma zazzayewar kasa da suka addabi China ya karu ya zuwa akalla mutane 400. A ranar juma´a ta makon jiya ruwan sama kamar da bakin kwarya hade da mahaukaciyar guguwa ta Taifun ta afkawa yankin kudu maso gabashin China. A halin da ake ciki an kwanshe mutane kimanin miliyan 3 zuwa tudun mun tsira.