1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ambaliyar ruwa a kasashen kudu maso gabashin Turai

April 17, 2006
https://p.dw.com/p/Bv1d

Tare da gina sabbin madatsun ruwa da sabbin hanyoyin karkata magudanar ruwa dubban mautane a yankin kudu maso gabashin Turai na kokarin tinkarar batsewar kogin Danube. A kasashen Romania da Bulgaria dubban ma´aikatan ceto da sojoji ke gudanar da wannan aiki. Ana sa rai nan da kwanaki kadan masu zuwa ruwan kogin zai kai wani matsayi da bai taba kaiwa ba. A Sabiya kuwa ruwan kogin ya fara janyewa, to amma a Belgrade babban birnin kasar ruwa ya malale wasu gine gine na tarihi.