1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ambaliyar ruwa a Indonisiya

Mutane fiye da 100 sun mutu 150 sun ɓata a cikin ambaliyar ruwa da mahaukaciyar guguwa a Indonisiya

default

Ambaliyar ruwan tsunami a Indonisiya

Mutane fiye da 100 sun rasa rayuka, sannan aƙalla 150 sun yi ƙasa ko sama, sanadiyar wata mummunan ambaliyar ruwa a ƙasar Indonisiya.Wannan ambaliya ta tsunami ta wakana kwana ɗaya rak bayan wani bila´in girgizar ƙasa a gaɓar tekun Sumatra, wadda ta haddasa rugujewar gidaje da dama.Mafi yawan asara ta wakana  a yankunan Pagai Utara da Pagai Selatan.

Cemma dai ƙasar Indonisiya ta saba da ire-iren wannan bila´o´i daga indallahi.

A halin da ake ciki gwamnati ta tura masu agaji kuma ta yi kira ga ƙasashen duniya su bata taimako cikin gaggawa.

Mawallafi: Yahouza Sadissou Madobi

Edita: Ahmad Tijani Lawal