Ambaliyar Ruwa a China | Labarai | DW | 08.08.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ambaliyar Ruwa a China

Sama da mutane 100 sun rasa rayukansu a China

default

Hukumomi a ƙasar China sun tabbatar da mutuwar mutane kimanin 100, a yayin da wasu dubu biyu suka ɓace sakamakon zabtarewar laka da ruwan sama kamar da baki ƙwarya ya haifar a garin Gansu da ke arewa maso yanmacin ƙasar. Kanfanin dillancin labaran Sin ya ruwaito cewar gidaje da dama ne suka nutse kana hanyoyi da dama suka yanke, a sakamakon ruwan saman kamar da baki ƙwarya. Tuni dai hukumomi suka sauyawa mutane dubu 45 matsuguni. Tuni primiyan ƙasar ta Sin Wen Jiabao ya shirya kai ziyara yankin da anbaliyar ruwan ya auku, tare da yin kira ga masu aiyukan ceto su gaggauta ceto mutane da wannan bala'i ya rutsa dasu.

Mawallafi: Babangida Jibril, Edita Zainab Mohammed