Ambaliyar ruwa a Brazil | Labarai | DW | 08.01.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ambaliyar ruwa a Brazil

Wani ambaliyar ruwan sama da aka dinga yi kamar daga bakin kwarya, yayi sanadiyar mutuwan mutane 50 a kasar Brazil.

Akasari mace macen ya fi shafuwan mutanen da ke zaune a yankunnan da ke da yawan tsaunuka a birnin Rio de Janeiro lokacin da gidaje suka dinga rushewa a sanadiyar yawan ruwan saman. Fiye da mutane dubu 15 suka rasa gidajen su a birnin Rio de Janeiro inji jami’an kungiyar tsaro ta kai. Bincike ya nuna cewar mai yuwuwa a samu karuwar ruwan saman cikin makonnin masu zuwa, an kuma kafa dokar tabaci a yankunnan da abin yafi shafuwa.