Ambaliyar ruwa a Asiya ta shafi wasu yankuna na gabacin Afurka | Siyasa | DW | 28.12.2004
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Ambaliyar ruwa a Asiya ta shafi wasu yankuna na gabacin Afurka

Daga cikin yankunan da ambaliyar ruwan da girgizar kasa ta haddasa a Asiya ta shafa har da wasu sassa na Somaliya da Kenya da Mauritius da kuma Seychells

Barnar da ambaliyar ruwa tayi a Asiya da wasu yankuna na Afurka

Barnar da ambaliyar ruwa tayi a Asiya da wasu yankuna na Afurka

A jiya litinin gwamnatin Somaliya ta ba da sanarwar cewar ba a san makomar wasu daruruwan masunta na kasar ba a yayinda ambaliyar ruwa tayi awon gaba da kauyukanta da dama. Wadannan masunta ba su dawo gida ba kuma bisa ga dukkannin alamu igiyar ruwa ce da ta samo tushe daga girgizar kasar da ta haddasa ambaliyar tekun pacific ta yi awon gaba da su, a cewar wani mai magana da yawun gwamnatin rikon kwarya kasar ta Somaliya, dake da mazauninta a kasar Kenya. Babu dai wani bayani dalla-dalla da aka samu, wanda ke tabbatar da wannan rahoto. A sakamakon kazamar girgizar kasar da aka fuskanta a tekun Indiya an samu cikowar ruwa ya zuwa gabacin Afurka dake a tazarar kilomita dubu bakwai daga cibiyar girgizar kasar. Su ma kasashen Kenya da Mauritius da tsuburan Seychells sun ba da sanarwa a game da irin barnar da ambaliyar ruwan tayi musu. Ita kuma kasar Tanzaniya a bayan kowace awa daya sai ta gabatar da gargadi ga masuntanta a game da igiyar ruwan da ka yi musu ba zata. An samu rahoton wani mutum daya a garin Malindi mai tashar jiragen ruwa da kuma wata matar da ta ji rauni tare da ‚ya’yanta guda biyu a Mombasa a kasar Kenya. A can Seychells kuwa igiyar ruwa tayi awon gaba da wata gadar dake sadarwa tsakanin garin Viktoriya mai tashar jiragen ruwa da filin saukar jiragen sama na kasar sannan a Mauritius ruwa ya mamaye wani kauye har tsawon sa’o’i da dama. Abin mamaki dai shi ne yadda bala’in ambaliyar ya fi shafar kasar Somaliya. Daya daga cikin dalilan dai shi ne kasancewar kasar tana can ne tozon gabar tekun baharmaliya kuma ba ta da mahukuntan da zasu iya ba da gargadi ga masunta da sauran mazauna kauyukanta, a sakamakon haka igiyar ruwan ta zo musu a ba zata. A kasar Kenya dai sanarwa ta ce al'amura sun fara sararawa kuma barnar ba ta taka kara ta karya ba, ko da yake an hango wasu masuntan dake kokarin tsamo jiragensu da ambaliyar tayi kaca-kaca da su daga cikin tekun. An kuma gabatar da gargadi ga masu sha’awar ninkaya da su yi taka-tsantsan saboda mahaukaciyar igiyar ruwa dake addabar gabar tekun kasar yanzu haka.