Ambaliyar Ruwa a Afrika | Labarai | DW | 26.09.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ambaliyar Ruwa a Afrika

Kungiyar bada agajin kasa da kasa ta red cross,tayi gargadi dangane da bukatar samarda agajin gaggawa na abinci wa kasashe yammaci da gabashin Afrika da suka fuskanci matsalar ambaliyar ruwa,kuma ke cigaba da kasancewa ciki.Headquatar kungiyxar Red Cross dake dake birnin Geneva ta bayyana halin kunci da Ghana da Sudan da Uganda ,wadanda ke cikin kasashe 22 da ke fuskantar ambaliyan ke ciki,inda akalla mutane million 1.5 ke bukatar tallafi.Kungiyar dai tace wannan ambaliyan ruwa ya lalata gonakin abinci,adangane da hakane ya dace kungiyoyi da hukumomin bada agaji su kasance cikin shirin kota kwana ,adangane da halin karancin abinci da zaa fuskanta a wadannan kasashen.