1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ambaliyar ruwa a ƙasar Habasha

August 9, 2006
https://p.dw.com/p/BunF

Maáikatan ceto a ƙasar Habasha sun cigaba a rana ta uku a ƙoƙarin gano mutane fiye da 300 waɗanda suka ɓace bayan mummunan ambaliyar ruwa wanda ya hallaka mutane fiye da 200 a ƙarshen mako. Jamián soji da yan sanda na cigaba da haƙar laka a garin Dire Dawa domin gano gawarwakin mutane waɗanda suka rasu a sakamakon tumbatsar ruwa daga kogin Dechatu. Baturen yan sanda na yankin Benyam Fikru ya shaidawa manema labarai cewa ya zuwa yanzu an gano gawarwakin mutane 210. yace an baza masu aikin ceto a tsawon daírar kilomita 35 a gabar kogin na Dire Dawa dake gabashin birnin Addis Ababa. Wasu mazauna yankin sun zargi gwamnati da rashin kafa ƙwaƙwaran shinge da zai kare ambaliyar ruwa. Suna cewa wannan ba shi karon farko da kogin yake barazanar ɓarkewa ba.