Ambaliya ruwan saman a ƙasar Chaina
June 17, 2010A ƙalla mutane 46 suka mutu yayi da wasu guda 50 suka ɓata a sakamakon ruwan sama kamar da bakin ƙwarya da ake sheƙawa a kudancin ƙasar Chaina waɗanda suka hadassa ambaliya.
Offishin ministan harakokin waje na ƙasar da ya baiyyana adadin mutanen da lamarin ya rutsa da su, ya shedda cewa tun a ranar lahadi an ƙwashe sama da mutane dubu 240 a cikin wasu garuruwa shidda na yankin kudancin na kasar yayin da gidaje kamar dubu 33 suka ruguje.
Ruwan saman dai da ake sheƙawa a kasar ba dare ba rana a 'yan kwanakin nan sun tilassawa hukumomin kula da al' amuran sufiri na kasar soke tashin jiragen sama 314 yayin da wasu tashin 489 aka ɗakasu haryazuwa wani lokaci.
Mawallafi: Abdourahamane Hassane.
Mawallafi : Abdullahi Tanko Bala.