1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ambaliya ruwan sama a ƙasar Ghana

Mutane a ƙalla guɗa 24 suka rasa rayukansu a sakamakon ruwan sama kamar da baƙin ƙwarya da aka ƙwashe ƙwanaki biyu ana yi a ƙasar

default

A sakamakon ruwan sama kamar da bakin ƙwarya da aka ƙwashe ƙwanaki biyu ana sheƙawa a ƙasar Ghana mutane a ƙalla guɗa 24 suka rasa rayukansu. .

Masu aikin agaji a ƙasar sun ce an samu gawarwaki guɗa 11 a Accra baban birnin ƙasar sanan wasu 13 a cikin sauran yankuna, sanan kuma ruwan saman sun lalata hanyoyi tare da kada gidaje.

Ambaliya ruwan dai ta shafi yankuna ukku na ƙasar a ciki hada birnin Accra inda lamarin ya fi tsananta.

Shugaban hukumar agajin gagawa na ƙasar Kofi Portuphy ya bayyana cewa ba mamaki naga ba adadin mutane da lamarin ya rutsa da su ya ƙaru .

Mawallafi: Abdourahamane Hassane

Edita : Mohammed Awal Balarabe