Ambaliya ruwa a Amirka ta Tsakiya | Labarai | DW | 31.05.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ambaliya ruwa a Amirka ta Tsakiya

Mutane aƙalla 96 suka mutu a sakamakon ruwan sama haɗe da iska mai ƙarfi a Amirka ta Tsakiya

default

Dutsin Pacaya da ke aman wuta a ƙasar Gwatemala da ya haɗasa ambaliya ruwa

Mutane aƙalla 96 suka mutu a sakamakon ruwan sama kamar da bakin ƙwarya haɗe da iska mai ƙarfi da aka riƙa yi da ake kiran Aghata a ƙasashen Salvador,da Honduras dakuma Guatemala, inda anan aka samu assara rayuka 83 yayin da wasu 20 suka yi ɓatan dabo.

Laka da ta riƙa zubowa a sakamakon dutsen dake yin aman wuta a yanki wato Pacaya ta share gidaje da itace dakuma duk, abinda ta samu akan hanyarta kamar yadda wasu shedu suka bayyawa kamfanin dillancin labarai na Faransa AFP.

Yanzu haka dai mutane kamar dubu tamanine a ka kwashe daga yankunan da lamarin ya fi ƙamari, sannan masu aikin ceto sun ce akwai yiwuwar ambaliya ruwan ta ƙaru a sanadin aman wuta da dutsin Pacaya ke yi, wanda ke a ƙasar Guatemala, kuma sannan sun ce aikin agajin na kai ɗauki ga jama´a dake a ƙawuka na gamuwa da cikas saboda tokar dake zuba daga dutsen.

Mawallafi :Abdourahamane Hassane.

Edita : Yahuza Sadisu Madobi