Ambaliya: Birtaniya za ta aika da karin sojoji
December 28, 2015Talla
Firaministan Birtaniya David Cameron ya bada sanarwar aikawa da karin sojoji 200 domin kawo dauki a yankunan Arewacin kasar da suka fiskanci ambaliyar da ta biyo bayan ruwan sama kama da bakin kwarya da aka share kwanaki ana shatatawa a yankin.
Da ma dai a baya gwamnatin ta aika da sojoji 300, amma kuma Firaminista Cameron ya ce akwai yiwuwar tura karin wasu sojojin dubu idan dai har matsalar ta kara kamari a nan gaba.
Kafofin yada labaran kasar ta Birtaniya dai sun ruwaito cewa a wannan Litinin Firaministan Cameron zai kai ziyara a yankunan da ambaliyar ta shafa.