1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ambaliya a kudancin Malasiya

Dubbannin alummomin kasar Malasia ne ke cigaba da samun mafaka a gine ginen gwamnati ,sakamakon ambaliyan ruwa na mako guda daya ritsa da kudancin kasar.Rahotanni daga Kuala Lumfur dai na nuni dacewa prime ministan kasar ya bayyana takaicinsa da yadda ake sace sacen kayayyakin jamaa a yankuna da aka samu ambaliyan ruwan.Kusan mutane dubu 70 ne ke samun mafaka a gine ginen gwamnati a jihar Johor dake kudancin Malasia,kana wasu dubu 10 na jihar Macca dake makwabtaka,ayayinda wasu kusan dubu 6 ke jihar Pahang dake gabashin wannan kasa.Prime minista Abdullah Ahmad Badawi yayi kira ga alummomin yankin dasu taimaka wajen cafke wadanda ke kokarin sace kayayyakin jamaa.Wannan ambaliyar dai na mai zama mafi munin irinsa ,wanda yazo bayan ruwan sama mai karfi.Kawo yanzu dai mutane 7 ne suka rasa rayukasnsua jihar ta Johar kadai.