Amadu Tumani Ture yayi tazarce | Labarai | DW | 03.05.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Amadu Tumani Ture yayi tazarce

Opishin ministan cikin gidan ƙasar Mali ya bayyana Amadu Tumani Ture a matsayin ɗan takara da ya lashe zaben shugaban ƙasa, da ya wakana ranar lahadi da ta wuce.

Sanarwar ta ce, shugaba Tumani Ture, ya yi tazarce tun zagaye na farko, tare da kashi 68 bisa 100, na yawan ƙuri´un da aka kaɗa.

Ibrahim Bubakar Keita, wato IBK,shugaban Majalisar dokoki, ya zo na 2, tare kashi kussan19 bisa 100.

Saidai gungun jam´iyun adawa, ya bayana aniyar shigar da kara kotu muddun hukumar zaɓe ta amince ta bayyana nasara shugaba ATT.

Jam´iyun adawar sun zargi ɓangaren shugaban ƙasa da tabka maguɗi.

Wakilan sa ido da ƙungiyar ECOWAS ta tura sun shaidi cewar zaɓen ya wakana lami lahia ,saidai yan matsalolin da ba za rasa ba nan da cen.

A cewar Kalla Mutari, ɗaya daga jami´an da su ka sa ido a wannan zaɓe, bisa dukkan alamu, ɗan takara da ya zo na 2, wato IBK, ba za shi dogowar jayyaya ba, a game da wannan sakamako.