Alwashin murkushe kungiyar IS | Labarai | DW | 23.03.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Alwashin murkushe kungiyar IS

Amirka da kawayenta kan rikicin yankin kasashen larabawa sun yi alkawarin kawar da kungiyar IS a Iraki da kewaye tare da barazanar kama shugaban kungiyar da ransa.

Kasashen da ke yaki da kungiyar IS karkashin jagorancin gwamnatin Amirka sun lashi takobin murkushe mayakan tarzoman IS a Iraki da sauran yankunan da suke, a lokacin wani taron da hankali ya karkata harin birnin London da kuma kisar fararen hula a kasar Syria.

Sakataren harkokin wajen Amirka Rex Tillerson, ya yi marhabin da azamar kasashe 68 na yankin larabawa da ke cikin gamayyar, tare da alkawarin farautar shugaban kungiyar ta IS Abubakar Al Bagadadi.

Sai dai fa yayin da suke ganawar a ma'aikatar harkokin wajen Amirka, sai aka sami labarin wani hari ta sama da sojojin gamayyar suka kai arewacin Siriya inda suka kashe fararen hula da dama.

Sakataren harkokin wajen na Amirka Mr. Tillerson, ya kuma gana da takwaransa na kasar Birtaniya Boris Johnson bayan taron, sai dai fa ba a yi wa ‘yan jaridu karin bayani ba.