1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Al'ummar Masar na zaben shugaban kasa

Zulaiha Abubakar
March 26, 2018

A yau ne al'ummar Masar ke gudanar da zaben shugaban kasa inda shugaba mai ci Abdulfatah Al-Sisi ke neman wani sabon wa'Adin mulki

https://p.dw.com/p/2uxXU
Ägypten Präsidentschaftswahlen
Hoto: Getty Images/AFP/K. Desouki

Za a dauki kwanaki uku ana zaben shugaban kasar a fadin kasar ta Masar. A baya dai jami'an tsaro sun kame da dama daga cikin wadanda suka bayyana aniyar su ta takarar neman kujerar shugabancin kasar, lamarin da ya haifar da samun abokin takara daya tilo Moussa Mustafa Moussa da ya iya dagewa a kan bukatar ja da Shugaba Sisi don neman shugabancin kasar.