Al′ummar Amirka za su sauya tarihin shugabanci | Labarai | DW | 08.11.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Al'ummar Amirka za su sauya tarihin shugabanci

Bayan lokaci na nuna wa juna yatsa 'yan takara Clinton da Trump a ranar Talatan nan al'umma za su yi alkalanci kan wanda zai jagorance su.

Mazauna wasu kananan yankuna uku na New Hampshire sun fita kada kuri'ar tsakar dare da misalin karfe biyar agogon GMT, wani zabe da ke nuna fara zaben shugaban kasa mai dinbin tarihi a Amirka.Yankin na Dixville Notch sun fara irin wannan zabe tun a shekarar 1960 yayin da yankunan Hart da Millsfield suka fara kada kuri'unsu a wasu lokuta fiye da rabin karni da ya gabata. Al'umma da ke a zaune a yankuna da ba jama'a sosai na da irin wannan dama ta kada kuri'a da wuri kana a rufe kada kuri'ar da wuri.

A jajiberin wannan zabe dai dukkanin 'yan takarar Clinton da Trump sun karkare gangaminsu yayin da su ke da dama ta bin gida gida dan jan hankali na masu zabe su fita kada kuri'a. Dubban magoya bayan Clinton a Philadelphia da Pennsylvania sun fita a gangami na karshe.