1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Al'ummar Afirka ta Kudu sun fita zabe

Yusuf BalaAugust 3, 2016

Jami'iyyar ANC da ke zama fitacciya ta tsohon Shugaba Nelson Mandela na fiskantar babbar barazana inda ake ganin za ta iya rasa kujeru a manyan birane.

https://p.dw.com/p/1JacG
Südafrika Wahlen Wahllokal 07.05.2014
Aikin zabe a Afirka ta KuduHoto: Reuters

A ranar Laraban nan ce al'ummar kasar Afirka ta Kudu ke fita zaben kananan hukumomi da ke zama mai zafi, jam'iyyar ANC mai mulki za ta iya shan kayi da ba ta taba gani ba tun bayan kawo karshen mulkin wariyar launin fata a wannan kasa.

Jami'iyyar ANC da ke zama fitacciya ta tsohon Shugaba Nelson Mandela na fiskantar babbar barazana inda ake ganin za ta iya rasa kujeru a manyan birane kamar birnin Pretoria da Johannesburg da Port Elizabeth kamar yadda kuri'ar jin ra'ayin jama'a ta nunar.

A yanzu da kasar ke fafutika ta kare kai daga barazanar tattalin arziki, ga yawan marasa aikin yi, manyan jam'iyyaun adawa kamar ta Democratic Alliance AD da ta masu fafutikar kare tattalin arziki ta EFF, ana ganin za su taka muhimmiyar rawa a wannan zabe da ke zama zakaran gwajin dafi na nuna bakin jinin jam'iyyar ANC tun bayan badakalar cin hanci da rashawa da ta mamaye mambobin jam'iyyar.