1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Al'umman Faransa sun ce "non", ga kundin tsarin mulkin Kungiyar Hadin Kan Turai.

YAHAYA AHMEDMay 30, 2005

Sakamakon zaben raba gardamar da aka gudanar a ran 29 ga watan Mayu na nuna cewa, masu adawa da kundin tsarin mulkin Kungiyar Hadin Kan Turai ne suka ci nasara. Ko wane irin hali Kungiyar za ta sami kanta a ciki a halin yanzu ?

https://p.dw.com/p/Bvbd
Masu adawa da kundin, suna murnar nasarar da suka samu a dandalin Bastille a birnin Paris, bayan an gabatad da sakamakon zaben.
Masu adawa da kundin, suna murnar nasarar da suka samu a dandalin Bastille a birnin Paris, bayan an gabatad da sakamakon zaben.Hoto: AP

Samun nasarar da `yan na ki suka yi, a zaben raba gardamar Faransa da aka gudanar a ran 29 ga watan Mayu, don amincewa ko kuma yin watsi da kundin tsarin mulkin Kungiyar Hadin Kan Turai, ba abin mamaki ba ne. Tun `yan makwanni kadan kafin a gudanad da zaben ne, masu binciken ra’ayin jama’a, suka bayyana cewa, mafi yawan `yan kasar ne ke nuna rashin amincewarsu da wannan kundin. Duk da hakan dai, shugabannin siyasa na nan Turai, ba su dau wannan kashedin da muhimmanci ba. Yanzu kuwa da sakamakon ya tabbatad da hasashen da aka yi, ba su kuma da wani zabi. A jiya da yamma, bayan an gabatad da sakamakon zaben, Jean Claude Junker, Firamiyan kasar Luxemburg, wanda kasarsa ce ke jagorancin Kungiyar Hadin Kan Turan a halin yanzu, da shugaban Hukumar Kungiyar, Jose Manuel Barroso, jawabai masu dumi-dumi kawai suka iya yi, inda suka ce za a ci gaba da aiwatad da manufofin samad da Turai guda daya.

Amma abin da masharhanta ke tambaya shi ne a ci gaba zuwa ina ? A halin yanzu dai, kasashe mambobin kungiyar, daya bayan daya, za su dinga gabatad da kundin tsarin mulkin ne ga zabe, ko a majalisun dokokinsu, kamar yadda Jamus ta yi, ko kuma ga al’umman kasar kamar dai yadda ya wakana jiya a Faransa.

A karshen bazara ta shekarar badi ne ake sa ran za a sami sakamamkon duk kasashen. Sa’annan ne shugabannin gwamnatoci da na kasashen kungiyar za su yi wani taron koli na musamman, don yin nazarin darussan da sakamakon ke dauke da su. To sai kuma me ?

A halin da ake ciki yanzu dai, ko da duk kasashen kungiyar ban da Faransa, sun amince da kundin, ba za a iya sake dawowa, a bukaci Faransawan su sake ka da kuri’un raba gardama ba. Kazalika kuma, ba za a iya sake kalmomin kundin ba, don faranta wa `yan wata kasa rai. Saboda idan aka ce za a yi haka, ko wace kasa ke nan za ta zo da bukatunta. To fa an shiga muhawara ke nan da ba ta da matuka.

Masharhanta da dama dai na gainin cewa, kundin, kamar yadda yake a yanzu, ba shi da wani muhimmanci kuma. Saboda, bisa ka’ida, ba zai taba zamowa doka ba, sai duk kasashen kungiyar sun amince da shi. Ga shi dai Faransawa sun juya masa baya da ka da masa kuri’ar na ki da suka yi. Wannan kawai ma ya isa, a yi watsi da shi gaba daya. Ba sai an jira sakamakon sauran zabukan raba gardamar da za a gudanar a wasu kasashen kungiyar, kamar a Holland ba, inda a ran laraba mai zuwa ne al’umman kasar za su ka da nasu kuri’un.

To yanzu ina Turai ta nufa ? Cikin tabargaza, kor udami, ko dai tabarbarewar al’amuranta ? Babu dai wanda ke sha’awar ganin cewa, wannan sakamakon ya janyo wa Turan wata annoba. Ko ba da kundin ba ma, kafofin kungiyar za su iya aiki, bisa ka’idojin da aka yarje a kansu tun da, kamar dai yarjejeniyar nan ta Nizza. Sai dai babu shakka, za a sami hauhawar tsamari. Amma a ganin, Günter Verheugen, mataimakin shugaban Hukumar kungiyar, wannan kalubale ne ga dukkan masu fada a ji a da’irar kungiyar, inda ya kamata su nuna bajinta, wajen tabbatad da cewa, duk da wannan cikas, za a ci gaba da aiwatad da manufofin hade kan Turan.

Kungiyar dai ba za ta wargaje ba, kuma za ta ci gaba da gudanad da ayyukanta. Bugu da kari kuma, Faransa ba za ta fice daga kungiyar ba, inji Verheugen.

A halin yanzu dai, abin da ya fi muhimmanci shi ne, shugabannin kungiyar su dau lokaci su yi nazarin ababan da ke hana mata ruwa gudu, sa’annan su yi gyaran kurakuran da suka yi. Bayan haka ne za su iya takalo batun samar wa duk kasashe mambobin kungiyar kundin tsarin mulki na bai daya.

Babu shakka, ko wadanne irin matakai aka dauka dai, za a sami bambancin ra’ayoyi game da neman da kasar Turkiyya ke yi na shiga cikin kungiyar. A yanzu, wasu na tantama, ko lalle ne za a fara shawarwari da Turkiyyan a ran 3 ga watan Oktoba, kan shigarta cikin kungiyar.

Da can dai, masu goyon bayan yunkurin Turkiyyan ne shugaba Jacques Chirac na Faransa, da shugaban gwamnatin tarayyar Jamus Gerhard Schröder. Amma sakamakon zaben na jiya, zai gurgunta matsayin shugaban na Faransa a shawarwarin kungiyar. Shi kuma Gerhard Schröder, shugaban gwamnatin Jamus, babu tabbas cewa, za a sake zabensa, a zaben majalisun tarayyar da za a yi a cikin watan Satumba mai zuwa.

Yanzu dai dai abin da zai fi dacewa ga Kungiyar Hadin Kan Turan ne, ta huskanci kalubalen da ke gabanta da kwazo, ta kuma nuna bajinta wajen shawo kan matsalolin da take huskanta.