1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zaben shugaban kasar a Venezuela

Suleiman Babayo MNA
May 20, 2018

Mutanen Venezuela na zaben shugaban kasa karkashin yanayi na matsalolin tattalin arziki gami da karancin kayan masarufi a kasar da ke yankin Latin Amirka.

https://p.dw.com/p/2y2IF
Venezuela Wahlen
Hoto: Reuters/C. Jasso

A wannan Lahadi al'umar kasar Venezuela ke zaben shugaban kasa, inda ake sa ran Shugaba Nicolas Maduro dan shekaru 55 ya sake samun sabon wa'adin shekaru shida, duk da matsalolin tattalin arziki da karancin kayayyakin masarufi gami da hauhawar farashin da ake samu a kasa.

A cikin shekarun da suka gabata fiye da mutane milyan guda suka tsere daga kasar saboda tabarbarewar harkokin rayuwa.

Shugaba Maduro zai yi lashe zaben saboda 'yan bangare adawa mafi karfi a kasar ta Venezuela da ke yankin Latin Amirka sun janye daga zaben, inda suke zargin shugaban ya mamaye komai babu alama bisa nuna gaskiya da adalci. Kana Henri Falcon da ke zama babban mai kalubalantan shugaban tsohon dan jam'iyya mai mulki ne wanda ba shi da karbuwa tsakanin galibin masu adawa da gwamnati.