Al′umar Ƙasar Poland suna cigaba da zaman makokin shugaba Kaczynski | Labarai | DW | 11.04.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Al'umar Ƙasar Poland suna cigaba da zaman makokin shugaba Kaczynski

Dubban 'yan ƙasar ne dai suka yi layi a gefen titin data tashi daga filin jirgin saman Warsaw, domin nuna alhini ga shugaban su mai shekaru 60 wanda ya rasu a wani hatsarin jirgin sama

default

Sojojin Poland ɗauke da gawar Shugaba Lech Kaczynski

A yau al'uman Poland sunyi tsit na mintuna biyu domin girmama shugaban ƙasar su Lech Kaczynski wanda aka kai gawar sa birnin Warsaw.

Dubban 'yan ƙasar ne dai suka yi layi a gefen titin data tashi daga filin jirgin saman Warsaw, har zuwa Fadar ta shugaban ƙasa domin nuna alhini ga shugaban mai shekaru 60 wanda ya rasu a wani hatsarin jirgin sama tare da  wasu 'yan ƙasar 96.

Yanzu haka dai bayanan da masu binciken musabbabin hatsarin jirgin sama na ƙasar Rasha suka fitar ya nuna cewar direban Jirgin yaƙi bin umarnin da aka bashi na dakatar da sauka da jirgin sakamakon rashin kyawon yanayi.

Tuni dai ƙasashen duniya da dama sukaci gaba da aikewa da saƙon su na alhini ga al'umar Poland, a birnin Berlin dake nan Jamus, Shugabar gwamnati Angela Merkel tace za'a saukar da tutocin Jamus ƙasa a ranar da za'ayi jana'izar shugaban na Poland, har yanzu dai ba'a baiyana ranar gudanar da jana'izar ba.

Mawallafi: Babangida Jibril

Edita: Zainab Mohammed Abubakar