Alqaida na kara fadada ayyukan ta a duniya inji Amurka | Labarai | DW | 12.01.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Alqaida na kara fadada ayyukan ta a duniya inji Amurka

Shugaban hukumar leken asiri ta Amurka, Mr John Negroponte yace, wasu shugabannin kungiyyar, Alqaida sun samu mafaka a kasar Pakistan.

Mr Negroponte, yaci gaba da cewa wannan sabuwar mafaka da jami´an kungiyyar ta Alqaida suka samu, ya basu damar kara daura damara a ayyukan su na ta´addanci.

A cewar babban daraktan , jami´an kungiyyar ta Alqaida a yanzu na samun ci gaban yaduwar kungiyyar su , a yankin gabas ta tsakiya da arewacin Afirka da kuma nahiyar turai.

Kusan a yanzu a cewar Mr Negroponte, kungiyyar ta Alqaida, kungiyyace, data kasance mafi girma dakewa duniya barazana. Barazana.

Idan dai an iya tunawa, a farko farkon wannan makon da muke ciki ne dakarun Amurka suka kaddamar da wani hari a somalia, da nufin halaka yan kungiyyar ta Alqaida ,da ake tunanin na da mafaka a kasar.