Alqaeda tayi kurarin kai sabbin hare hare a Amurka | Labarai | DW | 19.01.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Alqaeda tayi kurarin kai sabbin hare hare a Amurka

Kungiyyar Alqaeda tayi kurarin kai wasu sabbin hare hare a kasar Amurka. wannan kalamin dai na kunshe ne a cikin wani kaset da gidan talabijin na Aljazera ya yada a yau din nan, wanda aka danganta muryar dake cikin sa data shugaban kungiyyar ta alqeda, wato Usama Bin Laden .

Kaset din , wanda gidan talabijin din na aljazera ya yada mako guda bayan harin nan da dakarun sojin Amurka suka kai a Pakistan, muryar dake cikin kaset din ta kuma yiwa Amurkawa tayin tsagaita wuta bisa wasu sharruda.

Ya zuwa yanzu dai fadar mulki ta White House taki tace komai game da muryar dake cikin wannan kaset.

Sai dai a waje daya kuma , wani jami´i daga Amurka yace basu da tabbas cewa muryar dake cikin kaset din ta Usama Bin laden ce ko kuma a´a.